Hukumomin kasar Turkiyya sun tsare tsoffin hafsoshin sojin kasarta 10 bayan gamayyar wasu tsoffin Sojojin Ruwan kasar sun fitar da wata sanarwa da gwamnatin kasar ta alakanta da yunkurin juyin mulki a baya a kasar.
Kamfanin Dillancin Labaran Gwamnatin Turkiyya na Anadolu ya ce an tsare tsoffin hafsoshin sojin ne a ranar Litinin a wani bangare na binciken da Babban Mai Shigar da Kara na kasar ya kaddamarda kan wasikar da sojojin suka fitar.
Masu shigar da karar sun kuma umarci ragowar mutane hudun da ake zargi da su mika kansu ga ’yan sanda nan da kwana uku masu zuwa a maimakon a kama su, saboda shekarunsu.
Ana zargin tsoffin sojojin ne da yin amfani da karfi wajen tayar da zaune tsaye da kuma yunkurin juyin mulki.
Kamun dai na zuwa ne kwana daya bayan wata budaddiyyar wasikar da sama da tsoffin sojoji 104 suka fitar ta samu Allah-wadai daga Fadar Shugaban Kasar, wadda ta bayyana a matsayin burbushin masu yunkurin juyin mulki a baya.
An kuma tsare wadanda ake zargin ne a gidajensu da ke biranen Ankara, Istanbul da Kokacaeli kafin a gurfanar da su a ofishin Babban Mai Shigar da Kara na Kasar domin su fuskanci hukunci.