Dakarun Sojin Nijeriya sun fatattaki mayaƙan Lakurawa inda suka tattara komatsansu suka tsare zuwa Jamhuriyar Nijar.
Sanata Adamu Aliero ya sanar a safiyar Juma’a cewa a ranar Talata ne sojojin suka ragargaji mayaƙan na Lakurawa da suka shigo daga ƙasashen waje inda suka addabi al’ummomi a yankin Jihar Kebbi da Sakkwato da Zamfara.
Ya ce an samu wannan nasara ce a sakamakon matakan da Ministan Tsaro, Muhammadu Badaru Abubakar da manyan hafsoshin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki tsaki suka ɗauka kan mayaƙan.
A sanarwar da Aliero ya fitar, ya ce, “mun bayyana wa ministan ƙarara cewa, idan ba gaggauta ɗaukar matakin murƙushe Lakurawa, irin abin da ya faru na Boko Haram a Arewa maso Gabas zai sake faruwa a nan yankin Arewa maso Yamma.”
- Matsalar wuta: Ƙananan ’yan kasuwa sun sauya dabara
- An kama Akol Koor tsohon shugaban hukumar leken asirin Sudan ta Kudu
Dan Majalisar Dattawa ya shawarci ministan tsaron da ya ci gaba da tsaurara matakan tsaro don kada a koma ’yar gidan jiya.
A sakamakon hare-haren Lakurawa ne Sanata Aliero, wanda tsohon gwamnan jihar Kebbi ne, tare da wasu sanatoci suka ziyarci yankunan da abin ya shafa domin gane wa idonsu, inda suka ba da tallafin Naira miliyan 10 waɗanda abin ya shafa.