Sama da katan 1,958 na taliyar da darajarta ya kai Naira miliyan hudu da aka karkatar da ita daga jihar Binuwai ce ’yan sanda suka kama a Kano.
Taliyar na cikin wani bangare na katan 3,850 da gidauniyar Dangote ta bayar domin a tallafa wa marasa karfi a jihar ta Binuwai.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Habu Sani ya tabbatar da hakan yayin da yake jawabi ga ’yan jarida ranar Laraba a Kano.
Sai dai wanda ake zargin mai ya yi ikirarin cewa ya sayo takiyar ce daga hannun wadanda aka raba wa wanda ya ce ba sa bukatar tallafin.
Ya ce wasu daga cikinsu ma musayar shinkafa suka karba, wasu kuma suka karbi tsabar kudi kafin su bayar da taliyar.
’Yan sandan sun ce sun kama taliyar ce a kasuwar sayar da kayan masarufi da na abinci ta Singa da ke Kano.
– Masu garkuwa sun shiga hannu a Kano –
A wani labarin kuma, rundunar ’yan sandan Kanon ta kuma yi bajekolin mutum 259 da ake zargi da laifuka daban-daban da suka hada fashi da makami, garkuwa da mutane, satar motoci da babura masu kafa uku, kwacen wayoyi da dai sauransu.
Kwamishinan ’yan sandan ya ce Jami’an Sashen Rundunar na ‘Kan ka ce kwabo’ ne suka kama su a wurare daban-daban a fadin jihar cikin makonni shidan da suka gabata a kokarinsu na kakkabe bata-gari daga jihar.
Ya ce wadanda ake zargin sun hada da ’yan fashi 45, masu garkuwa da mutane 14, barayin motoci 14, barayin babura masu kafa uku guda bakwai sai kuma barayin mabura guda 14.
Sauran sun hada da mutum takwas da aka zarga da dillancin miyagun kwayoyi, ’yan damfara 28 da kuma ’yan daba 146.
CP Habu Sani ya kuma ce sun ceto mutane biyar da aka killace a dakuna ba bisa ka’ida ba da kuma kwace muggan makamai da miyagun kwayoyi daga hannun bata gari.