✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama sojan sama kan zarginsa da hannu a harin NDA

Za a tuhume shi ne kan bindigu da albarusan da aka yi amfani da su yayin harin.

An kama wani jami’in sojan sama, Sajan Torsabo Solomon, a Yolan Jihar Adamawa bisa zarginsa da hannu a harin da ’yan bindiga suka kai makarantar sojoji ta NDA da ke Kaduna.

A watan Agustan da ya gabata ne wasu ’yan bindiga suka kai hari makarantar, inda suka kashe sojoji biyu suka sace wani guda daya.

Sai dai daga bisani an ceto jami’in da aka sace din.

Rahotanni sun ce an kama Torsabo ne ranar Litinin, bisa umarnin Kwamandan Runduna ta 153 da ke Yola, bayan hukumomin sojojin a Kaduna sun bukaci hakan.

Wasu majiyoyi sun ce sojan dai, wanda ke aiki a wata makarantar sojojin sama da ke Yola, an wuce da shi Kaduna ne a wani jirgin sojoji mai lamba NAF 930 da misalin karfe 8:15 na dare.

Za a tuhume shi ne tare da bukatarsa ya amsa tambayoyi kan bindigu da albarusan da aka yi amfani da su yayin harin.

Da wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar ta 153 da ke Yola, Flight Laftanar Bayen, ya ki cewa uffan a kan batun inda ya ce zai yi karin bayani daga baya.

Sai dai har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton bai yi hakan ba.

To sai dai wasu majiyoyi daga rundunar sojojin saman sun tabbatar da kamen.

Sun kuma ce zargin jami’in da hannu a irin wannan harin ya girgiza ilahirin sojoji.