✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama sojan karya da bindiga da kakin sojoji a Kano

Mutumin ya dade yana musguna wa mutane a matsayin soja

An kama wani mutum da ya jima yana yaudarar jama’a da cewa shi babban soja ne mai mukamin Kyaftin a Kano dauke da kakin sojoji, bindiga da kuma albarusai.

Dubun mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, ta cika ne bayan ‘yan unguwar sun kai kararsa barikin sojoji na Janguza da ke jihar.

A cewar wani mutum, sojan gonan ya dade yana yawo a kan titin zuwa jami’ar Bayero yana karbar cin hanci daga hannun jama’a da sunan cewa shi jami’in soja ne mai mukamin Kyaftin.

A cewar wani wanda kamen sojan karyar ya faru a kan indonsa, sojan na karya na zaune ne a unguwar Danbare, ya kuma dade yana damfarar jama’a, a inda yake sa kayan soja masu dauke da sunan M.A Ibrahim a jiki.

Sojan na bogi ya shiga hannu ne bayan da ya je ofishin Hisbah ya kwato wata budurwarsa wacce suka kama a wani samame da suka kai wani wajen shaye-shayen a unguwar.

“Sojan karyan ya je da bindiga ofishin Hisba na Danbare inda ya harba ta sau uku a sama a cikin barazana, ya kuma tafi da budurwar tasa,” inji mutumin da bai amince a ambaci sunansa ba.

Ya kuma ce, “Mun je barikin sojoji na Janguza muka kuma aika musu da hotunansa sai suka ce ba su san shi ba, suka kuma ce duk inda muka gan shi mu fada musu”.

Bayan wani lokaci sai mutanen unguwar suka ga motarsa a wani gidan mai sai suka sanar da sojojin, a inda suka je suka kama shi tare da kayayyakin sojojin da suka kwace a hannunsa.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin barikin sojojin, amma wayarsa ta ki shiga.

Ya kuma tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya ce ya sami labarin, amma ba a mika musu mutumin da aka kama ba har lokacin hada wannan rahoto.