✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama sojan bogi mai damfarar ’yan mata a Legas

Ya yi wa wata mata fashi inda ya kwace mata mota kirar Lexus.

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta samu nasarar cafke wani sojan bogi da ake zargi da fashi da kuma damfarar ’yan mata a Jihar Legas.

Cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, rundunar ta ce dakarun bincikenta suka samu nasarar kama mutumin da ake zargin yana bayyana kansa a matsayin soja.

Rudunar ta ce sojan bogin mai shekara 39 yana bayyana kansa a matsayin dillalin tallata kayayyaki sannan ya gayyaci mata don gwada basirarsu.

A cewarta, sai dai daga karshen sojan bogin yana kwace wa ’yan matan kayayyaki ta hanyar ritsa da su bindiga.

Sanarwar ta ce an kama mutumin bayan daya daga cikin wadanda ya yi wa fashin ta kai rahoton kwace mata mota kirar Lexus RX330.

Binciken da rundunar ta gudanar ya gano karin wata motar alfarma da keken dinki da na’urar cire kudi ta POS a wajensa.

Rundunar ta nemi masu wadannan kayayyaki da su gabatar da kansu gare ta don karbar kayayyakinsu, inda ta ce za ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike a kansa.