✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama soja kan ƙoƙarin safarar alburusai a Borno

An kama sojan ne a tashar mota lokacin da yake ƙoƙarin safarar makaman.

Jami’an tsaro sun kama wani soja a tashar mota ta Borno Express da ke Maiduguri, a Jihar Borno kan zargin safarar alburusai ba tare da izini ba.

An gano cewa sojan, wanda ke aiki a runduna ta 7 da ke Maiduguri, yana ɗauke da harsasai 89 masu nauyin milimita 7.6 da aka ɓoye a cikin jakarsa.

Wannan abin ya faru ne bayan jami’an tsaro a tashar suka lura da halayensa, wanda hakan ya kai ga fara binciken cikin tsanaki.

Zagazola Makama, wani masani kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi, ya tabbatar da kamen sojan.

Ya bayyana cewa lamarin ya jawo damuwa kan yadda wasu ke cin amanar ƙasa.

Bayanai sun nuna cewa wanda ake zargin yana da alaƙa wajen yi wa ’yan ta’adda safarar makamai, wanda hakan na ƙara barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.

Hukumomin tsaro sun ce za su ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace don tabbatar da cewa babu wanda zai ci gaba da taimaka wa masu tada ƙayar baya da makamai ko kayan yaƙi.