An kama wani mutum mai shekaru 50 yana yi wa karamar yarinya mai shekaru hudu fyade a cikin wani masallaci a Jihar Bauchi.
Mutumin da a halin yanzu yake hannun ’yan sanda bayan jama’a sun lakada masa duka, sau biyu ana kulle shi a gidan yari saboda lalata kananan yara.
Wani shaida ya ce jama’a sun yi wa mutumin dukan kawo wuka bayan an kama shi ya yi wa yarinyar fayde, “wasu dattawa ne suka hana matasan kashe shi, amma an jibge shi sosai kafin isowar ’yan sanda”.
- An daura auren diyar Shugaban Kasa, Hanan
- Shigo da masara: Manoma sun fusata da Buhari
- Abin da ya yi wa Messi tarnaki a barin Barcelona
Ya ce mai fyaden ya yi wa yarinyar mummunan ranuni, “An garzaya da ita Asibitin Koyarwa da Jami’ar Abubakar Tafawabalewa domin kulawa da ita, saboda jinin da ke fita babu kakkautawa daga jikinta.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ta tabbatar da kama mutumin wanda ta ce a baya-bayan anan ne ya fito daga gidan yari a cikin fursunonin da Gwamntin Jihar ta yi wa afuwa a lokacin bullar cutar coronavirus.
Kakakin Rundunar, ASP Ahmed Mohmmaew Wakili ya ce, mutumin da ke zaune a uguwar Igbao Quarters, ya lalata yarinyar mai shekara hudu ne a wani masallaci da dake layin Aminu Stret.
Ya ce mutumin ya amsa cewa ya yi wa yarinyar fyade kuma ya taba aikata laifin a 2001 da 2015 har aka daure shi a kurkuku kafin a sako shi a cikin wadanda aka yi wa afuwa.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, CP Lawan Tanko Jimeta ya roki jama’ar jihar da su rika fallasa masu aikata miyagun laifuka ta hanyar taimaka wa ’yan sanda da bayanai.
Tuni dai Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta umarci Kwamitininta kan Harkokin Mata da ya bi kadin fyaden da aka yi wa yarinyar mai shekara hudu da mutumin ya lalata a cikin masallaci..
Majalisar ta wajabta wa Kwamitin bin shari’ar har zuwa karshe tare da tabbatar da doka ta ya halinta.
Shugabanta, Abubakar Suleiman tare da takwarorinsa sun yi tir da fyaden da aka yi wa yarinyar da kuma yadda ake samu karuwar matsalar.