✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama shi yana lalata da gawar buduwarsa da ya kashe zai yi tsafin kudi

Dubun wani matashi ta cika bayan da ya kashe budurwarsa ya yi ta lalata da gawarta na tsawon kwana shida da zummar yin tsafin kudi.…

Dubun wani matashi ta cika bayan da ya kashe budurwarsa ya yi ta lalata da gawarta na tsawon kwana shida da zummar yin tsafin kudi.

’Yan sanda sun cafke matashin mai shekar 36, wanda ake zargi da kashe budurwar tasa Precious Okeke mai shekara 24, wacce yake zaune tare da ita ne a unguwar  Badore da ke yankin Ajah Jihar Legas.

Ana zargin wani boka ne ya yi wa matashin tsafin kudi inda ya bukaci ya kashe budurwarsa ya sadu da gawarta har tsawon kwana bakwai.

Matashin ya yi ta yin tsubbace-tsubbacen da bokan ya sa shi tsawon kwanaki shida kafin dubunsa ta cika, bayan kwana shida da ya kashe budurwar tasa.

Makwabtan matashin ne suka ankarar da ’yan sanda bayan da warin gawar da ke fitowa daga dakinsa ya dame su, a lokacin ba su san abin da ke warin ba, sai bayan da ’yan sanda suka bincike dakinsa sannan suka gano aika-aikar da yayi.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce wanda ake zargin mai suna Ifeanyi Njoku ya yana hannun hukumar ’yan sandan tare da karin mutum guda da ake zargi da hannu a kisan budurwar mai suna Mbam Atumufor.

Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa an tisa keyar wadanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar da ke Panti a Yaba.