✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum uku a Jami’ar Ilorin bisa zargin fashi da makami

Wadansu mutum uku da ake zargin ’yan fashi da makami ne da suka dade suna addabar mutane a Jami’ar Ilorin sun shiga hannun ’yan sanda.…

Wadansu mutum uku da ake zargin ’yan fashi da makami ne da suka dade suna addabar mutane a Jami’ar Ilorin sun shiga hannun ’yan sanda.

Aminiya ta samu bayanin cewa, jami’an tsaron makarantar ce suka yi nasarar kama mutanen a lokacin da suke gudanar da aika-aikarsu a wani bangare na harabar jami’ar.

A yayin da yake bayyana abin da ya sani dangane da al’amarin, Mataimakin Jami’in Kula da Harkokin Dalibai na jami’ar, Dokta Aled Akanmu ya ce  mutanen jami’ar sun dade suna fuskantar masu fashi da makami, musamman ma cikin makonnin da suka gabata. Ya ce barayin kan shigo harabar jami’ar ce ta baya, musamman da dare, inda suke tare daliban da ke zuwa karatu a ajujuwan jami’ar, suna raba su da kayayyakinsu musamman wayoyin hannu da kwamfuta da sauran kaya masu daraja.

Ya ce “Mutanen uku, jami’an tsaron jami’ar ne suka kama su yayin da suke sintiri a harabar jami’ar. Suna sace wa dalibai kayayyakinsu, kuma sukan shiga ajujuwansu da dare dauke da adduna suna tsorata su. An mika mutanen da aka kama ga ’yan sanda kuma zuwa yanzu an gano dukan kayayyakin da suka kwace daga hannun dalibai, an mayar masu da abinsu.”

Jami’in ya kara da cewa a yanzu hukumar makarantar ta kara tsaurara matakan tsaro a jami’ar, inda aka hada har da gidajen kwanan dalibai da ke wajen jami’ar, musamman gidajen da suke da izinin sauke dalibai daga hukumar jami’ar.

Da yake karin bayani dangane da matakan tsaron da suka dauka, ya ce akwai wata cibiya da aka samar, wacce ke kula da gidajen dalibai da ke wajen jami’ar. Sun tanadar da lambobin waya, inda duk wani dalibi da ke bukatar taimakon gaggawa dangane da tsaro zai kira ya sanar da jami’an tsaron makarantar.