✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama mutum 83 bisa zargin aikata ta’asa a Binuwai

Mutane goma an kama su da laifin fashi da makami, 73 da laifukan ayyukan kungiyoyin asiri.

Rundunar ’Yan Sandan jihar Binuwai ta sanar da kame mutane 83 bisa zargin aikara ayyukan kungiyoyin asiri da kuma fashi da makami.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Mukaddas Garba ne, ya sanar da hakan ranar Talata a Makurdi, babban birnin jihar.

A cewarsa, 10 daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifin an kama su ne da ayyukan fashi da makami.

Ragowar 73 kuma in ji shi an kama su ne bisa zargin aikasta laifukan dake da alaka da kungiyoyin asiri.

Mukaddas ya ce kamen ya faru ne tsakanin 20 ga Disambar 2020 zuwa biyar ga Janairun 2021.

Ya kara da cewa an baza jami’an rundunar ‘yan sanda wuraren bukukuwa domin dakile ayyukan ta’addanci a jihar.

Kwamishinan ya kara da cewa rundunar ta sa, ta kwato bindigogi 15, adduna 20 da kuma harsasai da dama daga hannun ‘yan ta’addar.

Mukaddas ya kuma jinjinawa al’ummar jihar bisa yadda suke taimaka wa jam’ian tsaro da bayanan sirri wanda yake taimakawa sosai wajen nasarar rundunar.

%d bloggers like this: