✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke motocin abincin ’yan bindiga da mutum 100 a Zamfara

An kama akalla mutum 100 bayan kafa sabbin dokokin dakile ’yan bindiga.

Gwamnatin Zamfara ta kama wasu motoci makare da abinci  da man fetur a hanyarsu ta kai wa ’yan bindiga a sansanonin da ke cikin dazukan jihar.

Gwamnatin ta kara da cewa sama da 100 sun shiga hannu kan saba dokar rufe kasuwannin dabbobi da haramta zirga-zirgar ababen hawa bayan karfe 10 na dare da sauran dokokin da ta sa da nufin dakilye ayyukan ’yan bindiga a Jihar.

Sakataren runduna ta musamman da gwamnatin jihar ta kafa domin yaki da garkuwa da mutane da kuma tabbatar da bin dokar, Abdulrasheed Haruna, ne ya sanar da haka.

Ya ce an mika mutanen da suka shiga hannu ga hukumomin tsaro domin su bincike su sannan su gurfanar da su a gaban kotuna.

Haruna ya ce rufe gidajen mai da kasunnin mako-mako a jihar sun kassara hanyoyin samun abinci da man fetur da sauran bukatun ’yan bindiga.

“Sun tilasta musu tserewa su bar jihar,” inji Haruna wanda ya ce rundunar ta kafa kananan kwamitoci 11 domin tabbatar da bin dokokin.

’Yan bindiga: Gwamnatin Zamfara ta rufe karin hanyoyi da kasuwanni

Kwamishin Yada Labaran Jihar, Ibrahim Dosara ya ce gwamnatin jihar ta dauki karin matakan tsaro a wasu yankuna.

Sabbin matakan su hada da “Rufe kasuwar Yargaya da ke Tudun Wada a Gusau, sai Mahadar Kaura Namoda zuwa Jibiya, da Marabar  Lambar Bakura, sannan Mahadar Colony zuwa Rini da kuma hanyar Mayar zuwa Anka,” inji shi.

A ranar 26 ga watan Agusta ne Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya kafa dokar rufe kasuwannin mako-mako da kuma zargi-zirgar ababen hawa daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe.

Dokar ta haramta goyo fiye da kima a kan babura da kekuna da kuma amfani da su daga karfe 6.30 na yamma zuwa 6.00 na safe a garin Gusau, a sauran wurare kuma daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe.

“Gaba daya an haramta jigilar dabbobi, hakazalika jigilar ice daga daji, da kuma sayar da man fetur a yankunan da ke karkashin masu unguwanni.

“An haramta sayar da man fetur a cikin kowane irin mazubi, sai dai abin hawa, kuma ba za a sayar wa abun hawa daya fiye da lita 40 na fetur ba.

“An kuma rufe kowadanne irin shaguna da rumfuna da tebura da ke Garejin Mailaina, a garin Gusau.