✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mota makare da makamai da aka shigo da ita Najeriya daga Mali

Ana kokarin kai makama Jihar Anambra ne lokacin da aka kama su

Dakarun bataliya ta 192 da ke runduna ta 81 ta kama wata mota makare da wasu makamai da aka shigo da su Najeriya daga kasar Mali, da nufin wucewa da su Jihar Anambra.

Jami’an rundunar dai da ke aiki a kan hanyar Ajilete-Owode da ke Karamar Hukumar Yewa ta Arewa a Jihar Ogun ne suka kama mutanen.

Kakakin sojojin kasa, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Ya ce an kama motar ce mai lamba ENU 697 XY, wacce ke dauke da fakiti 720 na da manyan bindigu 12.

Nwachukwu ya kuma ce akwai bindigu 25 a kowanne fakiti, wanda jimillarsu ya kai guda 18,000, sai kuma karin wasu guda 10 da ke dauke fakiti 10 makamai 2,500, dukkansu an kwace su nan take.

Kakakin ya ce wadanda aka kama din sun hada da wani dan kasar Ghana mai suna Eric Seworvor, da direbansa, Lukman Sani wadanda yanzu haka suke tsare, kuma ana ci gaba da bincike a kansu.

Ya kuma ce, “Bayanan da muka samu yayin bincikenmu na farko-farko sun nuna cewa makaman an kunshe su ne a cikin wata mota da aka shigo da ita a matsayin babu komai a cikinta daga kasar Mali, ta hanyar bodar Idiroko, inda motar ta tsallake shingayen bincike da dama, a kokarinta na zuwa Onitsha, a Jihar Anambra.

“Sakamakon daukar matakin da dakarunmu suka yi cikin gaggawa, Allah Ya taimake mu mun kama su, da ba don haka ba da haka za a shigar da wadannan makaman a je ana kashe mutanen da ba su ji ba,ba su gani ba,” in ji Nwachukwu.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da tallafa wa sojoji da ma sauran jami’an tsaro da ingantattun bayanai domin samun nasarar.