✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama maza 6 da laifin cin zarafin mace a Saudiyya

Yanzu suna fuskantar hukuncin daurin shekara kusan 10 a gidan yari.

Wasu maza shida sun shiga hannu kan laifin cin zarafin wata mace yayin da take ziyara a Riyadh, babban birnin Saudiyya.

An kama mazan ne kan laifukan da sai a shekarun baya-bayan aka fara hukunci a kansu, a cewar wani mai shigar da kara a ranar Litinin.

“An fara bincike a kan wasu ’yan kasa shida da suke cikin shekarunsu na 20 kan wani abu da ya faru.

“An zargin sun zagaye motar wata ’yar yawon bude ido suka ci zarafinsu da kalamansu da kuma dabi’un da suka nuna,” kamar yadda mai shigar da kara ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasar SPA.

An kama mutum shidan da ake tuhuma, wadanda sun amsa laifin nasu, kuma an tsare su yayin da ake ci gaba da bincike a cewar majiyar.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, a yanzu suna fuskantar hukuncin daurin shekara kusan 10 a gidan yari kan laifin, a cewar majiyar.

A baya-bayan nan aka fara kokarin magance matsalar cin zarafi a Saudiyya.

A watan Mayun 2018 gwamnati ta ayyana cin zarafi a matsayin laifi tare da hukuncin shekara biyar a gidan yari da kuma tarar riyal 300,000.