✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matsafi da sassan jikin mutum

Dubun wani matsafi mai suna Abdullatif Kayode da ke tu’ammali da sassan jikin bil Adama ta cika a Jihar Legas, a lokacin da rundunar ’yan…

Dubun wani matsafi mai suna Abdullatif Kayode da ke tu’ammali da sassan jikin bil Adama ta cika a Jihar Legas, a lokacin da rundunar ’yan sanda a jihar suka yi masa kwantan ɓauna a ranar Talatar da ta gabata, a sakamakon bayanan sirri da suka samu dangane da aikace-aikacen da yake gudanarwa a Unguwar Badare da ke yankin Alakuko, Legas.

Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Legas Edgal Emohimi ya shaida wa Aminiya cewa a lokacin da ya jagoranci jami’an ’yan sanda zuwa zauren da matsafin ke gudanar da aikace-aikacensa, sun ga sassan jikin mutane a cikin ƙaramar robar fenti. “Matsafin ya shaida mana cewa sassan jikin mutum ɗin sun haɗa da zuciyar mutum namiji, sai hanji da cinyar mace tare da al’aurarta, ya kuma ba mu bayanan wani babban matsafin da suke yin aikin tare; kodayake a lokacin da ya kai mu gidan wancan, ya riga ya samu labarin zuwanmu, ya tsere. Sai dai jami’anmu sun kame shi cikin mintuna 30 da barin gidansa,” inji shi.

Kwamishinan ya ƙara da cewa sun yi nasarar kame matsafan ne sakamakon tsarin nan na yin aikin ’yan sanda tare da jama’ar jihar, tsarin da ya ce yana taimakonsu wajen kakkaɓe miyagun ayyuka, sakamakon bayanan da suke samu daga wajan jama’a. Ya kuma shawarci jama’ar ’yankin da su kasance masu sanya idanu a kan mutanen da ke gewaye da su.