✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama matashin da ya yi garkuwa sannan ya kashe yaro mai shekara 5 a Kano

Sun kuma nemi iyayen yaron su ba su N20m bayan sun kashe shi

Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai shekara 29 tare da wasu mutane uku bisa zarginsu da yin garkuwa da kuma kisan wani yaro mai shekara biyar da haihuwa.

Daga baya kuma wadanda ake zargin sun nemi Naira miliyan 20 daga iyayensa a matsayin kudin fansa.

Kakakin rundunar a Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Kano ranar Alhamis.

Kiyawa ya ce mahaifin yaron ne ya shigar da korafi gaban ’yan sandan inda ya ce bayan sace dan nasa ne masu garkuwar suka nemi Naira miliyan 20, inda a karshe aka karkare a kan Naira miliyan biyar.

Kakakin ya kuma ce tun daga wannan lokaci Kwamishinan ’Yan Sandan na Jihar Kano ya baza jami’ansa zuwa wurare daban-daban, inda daga karshe aka kama shi a garin ’Yantama da ke yankin Karamar Hukumar Doguwa a Jihar Kano.

“Kokarin da jami’anmu suka yi shi ne ya bayar da damar har aka kai ga kama shi a maboyarsa.”

Kiyawa ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa don haka ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya don girbar abin da ya shuka.

A yanzu haka dai wasu fusatattun matasa sun kone gidajen wadanda ake zargi da kisan yaron.