Rundunar ‘yan sandan Jihar Oyo ta kama wani mai garkuwa da mutane mai suna Olarinde Adekunle da ya yi barazanar sace dalibai uku na wata Jami’a mai zaman kanta a jihar.
A ranar Litinin ce rundunar da kama Adekunle mai shekara 37 wanda ya aike wa jami’ar wasikar kwana da sanin cewa zai yi garkuwa da dalibanta uku.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya ce barazanar kamar yadda aka yi zato, ta kawo cikas ga harkokin ilimi a jami’ar, lamarin da ya haifar da firgici da rashin tabbas a tsakanin al’ummar jami’ar.
Adewale ya ce, ya yi farin cikin samun nasarar kama wanda ake zarigin kuma shi ne wanda yake barazanar kai wa wani sabon banki farmaki da ke Unguwar Owode a Oyo.
Jami’in dan sandan ya ce, “Wata fitacciyar kungiyar masu garkuwa da mutane ta aike da takardar da aka rubuta da hannu zuwa ga mahukuntan wata jami’a mai zaman kanta a garin Oyo, inda suka yi barazanar sace dalibanta uku idan har hukumar ta kasa biyan Naira miliyan 10 cikin wa’adin da aka kayyade.
“Wannan ya sa muka gudanar da bincike mai zurfi, kuma a dalilin haka aka kama wani Azeez Mufutau ‘M’ wanda lambobin wayarsa ke a rubuce a cikin wasikar da aka rubuta da hannu wanda aka aike wa mahukuntan jami’ar da kuma bankin.
“Da aka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya tabbatar da cewa lambar wayar da ke cikin takardar tasa ce, amma ya musanta cewa shi ne marubucin takardar.”