✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matashin da ake zargi da kashe budurwarsa

'Yan sanda a jihar Ogun sun cafke wani matashi mai suna Rexlawson Johnson bisa zargin kisan budurwarsa Patricia John.

‘Yan sanda a jihar Ogun sun cafke wani matashi mai suna Rexlawson Johnson bisa zargin kisan budurwarsa Patricia John.

Ana dai zargin matashin ne mai kimanin shekaru 31 da aikata laifin sannan ya cika wandonsa da iska.

Rahotanni dai sun ce Rexlawson ya kashe budurwar tasa a otal din Ibafo dake karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce manajan otal din ne ya kira su tare da tabbatar musu da samun gawar mace a ciki.

Kakakkin ya ce, “An samu ranuka a wuyan gawar yarinyar, wanda hakan ya nuna tasha wahala kafin ta rasu.

“Bincikenmu ya gano cewa yarinyar ta shiga Otal din tare da wani matashi, amma ya tsere bayan kashe ta.

“Bayan gudanar da bincike mun gano matashin da ya yi kisan, bayan tuhumarsa ya bayyana cewa sun samu sabani ne tsakaninsa da budurwa tasa,” inji Oyeyemi.

Bincike ya bayyana matashiyar mai shekaru 26 da haihuwa ta rasa ranta ne sakamakon duka da kuma raunuka da saurayin ya yi mata.