✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matashi zai saci janareta a kotu

An cafke shi ne a daidai lokacin da yake kokarin yin awon gaba da janaretan.

An cafke wani matashi a daidai lokacin da yake kokarin sace janareta a wata kotu a yankin Karamar Hukumar Ado-Odo Ota a Jihar Ogun.

Majiyarmu ta ce magatakardan kotun, Kareem Tolulope, da kansa ya damke matashin.

Bayanai sun ce a ranar Talata wanda ake zargin ya kutsa cikin ofishin da aka ajiye janaretan da zummar zai yi awon gaba da shi

A cewar majiyar, matashin ya yi amfani da damar hutun aikin da aka bai wa ma’aikata don zuwa karbar Katin Zabensu wajen aikata laifin.

Abubuwan da aka samu a jikinsa sun hada da wata ‘yar jaka da sukundireba.

Ya zuwa hada wanna labari, an kasa samun mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, balle a ji ta bakinsa kan batun.