✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matar da ke sojan gona a fadar shugaban kasa

Hukumar Tsaron Kasa ta Farin Kaya (DSS) ta gabatar da wata mata mai suna Amina Mohammmed wadda aka fi sani da Justina Oluoha ko Amina…

Hukumar Tsaron Kasa ta Farin Kaya (DSS) ta gabatar da wata mata mai suna Amina Mohammmed wadda aka fi sani da Justina Oluoha ko Amina Billa ga ’yan jarida kan zarginta da bayyana kanta a matsayin matar Gwamnan Jihar Kogi, Rashida Bello inda take amfani da fadar Shugaban Kasa domin damfarar jama’a.

Kakakin Hukumar DSS, Peter Afunaya, ya ce matar ta rika shiga cikin gidan matar Shugaban Kasa A’isha Buhari, kuma ce ta rika amfani da sunaye daban-daban domin shiga cikin fadar Shugaban Kasar. Hukumar DSS ta kama Amina Mohammed ce bayan an kama ta da laifin yin amfani da ofishin Uwargidan Shugaban Kasa, A’isha Buhari tana damfarar mutane

Sai dai Kakakin Hukumar DSS  din ya ce ana zargin matar da damfarar wani dan kasuwa mai suna Aledander Okafor da ake kira Chicason har Naira miliyan 150 a shekarar 2017, inda ta shigar da shi ofishin matar Shugaban Kasar a lokacin da ta tafi aikin Umara. Afunanya ya ce Amina takan fake da ministoci da jami’an fadar wajen samun shiga fadar Shugaban Kasa, kuma tana amfani da sunaye daban-daban wajen kauce wa binciken jami’an tsaro.

Amina ta musanta zargin da ake yi mata inda ta ce da sanin wata ’yar uwar matar Shugaban Kasa mai suna Mariatu da kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal take gudanar da harkokinta na sayar da wasu kadarorin gwamnati .

Sai dai Kakakin Hukumar DSS da Mai tallafa wa A’isha Buhari kan harkokin watsa labarai Sulaiman Haruna sun ce ba su da tabbacin ko ’yar uwar A’isha Buhari, Mariatu na cikin wadanda suke da alaka da laifuffukan da ake zargin Amina.

Lamarin na zuwa ne bayan watan uku da aka zargi jami’in tsaron Hajiya A’isha Buhari da amfani da sunanta wajen karbar makudan kudade daga wurin mutane, inda ake ci gaba da bincike a kai.