Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas, ta kama wata mata da ta kware wajen fataucin kananan yara daga Arewacin Najeriya zuwa jihar.
Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin ne, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, a ranar Lahadi.
Ya ce matar na amfani na wata kungiya wajen fataucin kananan yara daga Arewa zuwa Jihar Legas don yin ayyukan da suka saba wa doka.
“A ranar 25 ga watan Janairu, wata shugabar kungiya mai shekara 45 da ke zaune a kauyen Molete da ke Ilorin, ta shiga hannun ‘yan sandan Legas.
“An ceto kananan yara uku, mata biyu da kuma namiji daya daga hannun matar.
“Wadda ake zargin ta amsa laifin da ake tuhumarta. Kazalika bincike ya nuna cewa ta yi safarar kananan yara 42 zuwa Jihar Legas, don yin aiki ba tare da izinin iyayensu ba.
“Sannan rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara na zargin ta da laifin bacewar wasu yara a hannunta,” in ji shi.
Hundeyin, ya ce rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara, ta tabbatar da kwato wasu kananan yara 11 daga hannunta, amma ta tsere kafin ta shiga hannu.
Wadda ake zargin ta bayyana wuraren da ta ke kai yaran idan ta yi safarar su.