Sojojin Birget ta 6 a Jalingo Jihar Taraba sun kama wasu mutane takwas da ake zargin cewa ’yan Boko Haram ne a garin Sunkani hedikwatar Ƙaramar Hukumar Ardo-Kola.
Har wa yau kuma sojojin sun kama wasu mata su biyu da bisa zargin bai wa masu garkuwa da mutane bayanai kan masu kuɗi a yankin Ƙaramar Hukumar Takum ta jihar.
Muƙaddashin kakakin rundunar, Kyaftin Oni Olubodunde ya ce an damƙe mutunen ne a ranar Litinin a gidan wani wanda ake zargin ɗan Boko Haram ne a garin na Sunkani, bayan samun bayanai na sirri.
Kyaftin Oni ya ce binciken da aka gudanar ya nuna gano mutane suna shirye -shiryen kafa wata matattarar ’yan Boko Haram ne a garin na Sunkani tare da haɗa ababen fashewa da kai hare-hare sassan a Jihar Taraba.
Ya ce mai gidan da aka kama ya shaida wa sojoji cewa ya daɗe da shiga kungiyar Boko Haram tare da kaninsa wanda a halin yanzu yake cikin daji tare da sauran ’yan ƙungiyar.
Ya ƙara da cewa a ranar Litinin an kama wasu mata biyu a garin Chanchangi suna bai wa masu satar mutane bayanai kan masu dukiya a yankin.
Ya ce ana kyautata zaton mata ce da ƙanwar wani ƙasurgumin mai satar mutane wanda ake kira Anyogo .
Ya ce aikin matan shi ne bai wa ’yan bindiga bayanai kan ’yan kasuwa da masu kuɗi da zirga -zirgar jami’an tsaro a yankin.