✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mata ’yan leƙen asirin ’yan bindiga da ’yan Boko Haram a Taraba

Sojoji sun kama wasu mutane takwas da ake zargin cewa ’yan Boko Haram ne a garin Sunkani

Sojojin  Birget ta 6 a Jalingo Jihar Taraba sun kama wasu mutane takwas da ake zargin cewa ’yan Boko Haram ne a garin Sunkani hedikwatar Ƙaramar Hukumar Ardo-Kola.

Har wa  yau kuma sojojin sun kama wasu mata su biyu da bisa zargin bai wa masu garkuwa da mutane bayanai kan masu kuɗi a yankin Ƙaramar Hukumar Takum ta jihar.

Muƙaddashin kakakin rundunar, Kyaftin Oni Olubodunde ya ce an damƙe mutunen ne a ranar Litinin a gidan wani wanda ake zargin ɗan Boko Haram ne a garin na Sunkani, bayan samun bayanai na sirri.

Kyaftin Oni ya ce binciken da aka gudanar ya nuna gano mutane suna shirye -shiryen kafa wata matattarar ’yan Boko Haram ne a garin na Sunkani tare da haɗa ababen fashewa da kai hare-hare sassan a Jihar Taraba.

Ya ce mai gidan da aka kama ya shaida wa sojoji cewa ya daɗe da shiga kungiyar Boko Haram tare da kaninsa wanda a halin yanzu yake cikin daji tare da sauran ’yan ƙungiyar.

Ya ƙara da cewa a ranar Litinin an kama wasu mata biyu a garin Chanchangi suna bai wa masu satar mutane bayanai kan masu dukiya a yankin.

Ya ce ana kyautata zaton mata ce da ƙanwar wani ƙasurgumin mai satar mutane wanda ake kira   Anyogo .

Ya ce aikin matan shi ne bai wa ’yan bindiga bayanai kan ’yan kasuwa da masu kuɗi da zirga -zirgar jami’an tsaro a yankin.