✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mata ’yan bindiga a Abuja

An kama matan ne tare da gungun wasu maza hudu da ke addabar Abuja.

’Yan sanda sun kama ’yan bindiga mata biyu tare da gungun wani jagoran ’yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Abuja.

An kama matan ne tare da gungun wasu maza hudu da ke addabar Abuja a maboyarsu da ’yan sanda suka kai samame.

Sanarwar da Kakakin Rundunar, SP Josephine Adeh ta fitar ta ce, wadanda ake zargin ciki har da wani jagoran ’yan bindiga Buhari Muhammad, wanda ake nema ruwa a jallo, an kama su ne a wani otel da ke kauyen Bassa a Abuja.

SP Josephine Adeh ta ce, gungun ne suka yi garkuwa da wani Joshua Eze, wanda matarsa Blessing ta samu raunin harsashi a yayin da ake kokarin sace shi a ranar 27 ga watan Janairu, amma daga bisani ’yan sanda suka kubutar da shi washegari.

Sanarwar ta SP Josephine Adeh ta ce, an kwato bindiga kirar AK47 guda daya da wayoyin hannu 10 da kudi Naira 345,000 da wasu kayayyaki masu daraja daga hannun wadanda ake zargin.

Ta kara da cewa, tuni wadanda ake zargin suka amsa laifin da suka aikata da kuma wasu laifuka na garkuwa da mutane a yankin.

A cewar sanarwar, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, Kwamishinan ’Yan sandan Abuja, Benneth C. Igweh ya tabbatar wa jama’a kudirinsa na kawar da masu aikata manyan laifuka daga Abuja.

Kakakin ta bukaci mazauna yankin da su bayar da rahoton abubuwan da ba su yarda da take-takensu ba ga wadannan layukan karta-kwana 08032003913, 08061581938, 07057337653, da 08028940883; 0902222352.