✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama masu yankan aljihu 3 a wajen Babban Taron APC

An dai kama mutanen ne lokacin da suke karbe wa mutane wayoyinsu a kofar shiga filin taron

Jami’an tsaro sun cafke wasu masu yankan aljihu mutum uku a wajen Babban Taron jam’iyyar APC da ke gudana a Babban Birnin Tarayya Abuja.

An dai kama mutanen ne lokacin da suke karbe wa mutane wayoyinsu a kofar shiga filin taron na Eagle Square.

Wani jami’in tsaro da ya nemi a dakatar sunansa ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa barayin sun yi amfani da yanayin da ake ciki na cunkoso a kofar shigar ne wajen kwace wayoyin mutanen.

Ya ce, “Mutum ukun tafiyarsu daya, suna kwace wa mutane kudi da wayoyi sakamakon cunkoson da ke kofar shiga wajen taron.

“Abin da ya faru ke nan. Amma wani jami’inmu ya kama su bayan sun fara aika-aikar,” inji shi.

Jami’in tsaron ya ce za a wuce da wadanda ake zargi hedkwatar ’yan sanda ta kasa don fadada bincike a kan su. (NAN)

 

#APCNationalConvention #BabbanTaronAPC #TaronAPCNaKasa