Hukumar yaki da safarar mutane (National Agency for the Prohibition of Trafficking in Person) da aka fi sani da sunan NAPTIP, ta kama wasu mutane biyu daga Jihar Kano, a lokacin da suke shirin safarar wasu mata 14 da kuma maza 2 zuwa kasar Saudiyya a filin jirgin sama na Abuja.
Matan wadanda wakilinmu ya yi kicibis da su sun yi cirko-cirko a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litinin da ta gabata, sun tabbatar masa da lamarin, kamar kuma yadda hukumar ta bakin jami’in hulda da jama’a Mista Josiah Emerol ya tabbatar.
Jami’in ya bayyana cewa mata 14 da kuma maza 2 da shekarunsu ya fara daga 14 zuwa 50, mata 11 daga cikinsu sun fito ne daga garin Daura a Jihar Katsina, a yayin da mace guda ta fito daga garin Lafiya a Jihar Nassarawa, sai wasu karin mata biyu, daya daga Bachirawa Jihar Kano, dayar kuma daga garin Birnin Kudu Jihar Jigawa, sannan mazaje biyu daga kananan hukumomin Sabon Gari da kuma Zariya Jihar Kaduna.
Jami’in ya ce hukumar na kula da mutane 16 a sansaninta na kula da mutane da ke Abuja inda take yi masu nasihohi tare da ci gaba da zakulo bayanai daga wajensu, bayan ta ceto su a ranar Alhamis ta makon jiya a filin jirgin sama na Abuja. “Su kuma wadanda ake zargi da safararsu, wadanda maza ne daga Jihar Kano, suna hannun jami’an tsaro na DSS suna yi masu bincike gabanin gurfanar da su a gaban kotu a nan gaba,” inji jami’in hukumar.
Hukumar ta yi zargin cewa da dama daga cikin kungiyoyin da ke safarar mutane zuwa ketare, suna yaudarar wadanda suka fada komarsu ne da cewa za su sama masu aiki mai gwabi a kasashen waje, amma a karshe sai su jefa su cikin ayyuka da suka hada da bauta da karuwanci ko ayyukan hidimar gida fiye da kima, ko auren dole ko sanya su suna rawa a gidajen masha’a, ko daukarsu a fina-finan batsa suna sayarwa, sai kuma cire sassan jikinsu kamar su koda, wadanda a wani zubin suke sayarwa.
Ya ce yawancin wadanda aka fita da su din, ba su da takardun zama a kasashen kuma a dalilin hakan sai su ci gaba da fuskantar ukuba a wuraren da suke boye, kasancewar suna tsoron fitowa fili don kai maganar a gaban hukuma ko kuma ofisoshin jakadancin kasashensu da ke waje; kasancewar suna tsoron jami’an tsaron kasashen na iya kama su.