Wasu masu gadin makabarta biyu sun shiga hannu inda aka kama su da kawunan dan Adam da suka hoto da cikin kabari.
Dubunsu ta cika ne bayan mutanen unguwa suka kama daya daga cikin mutanen [da ake kira Alhaji] da kawunan mutane a cikin jika.
- Tsoron iyayenmu na hana maza neman aurenmu —’Yan matan barikin soja
- Ramadan: Ba ma bin ganin watan Saudiyya —Sarkin Musulmi
- An kama kwarto ya haka ramin da ke kai shi gidan auren tsohuwar budurwarsa
- An kai daraktan Kannywood Ashiru Nagoma asibiti
Wani mazaunin unguwar ya ce, “Jiya (Lahadi) da safe wani ya shiga jeji yin ba haya shiya sai ya ga Alhaji da wata katuwar guduma yana fasa wani kabari.
“Daga baya da Alhaji ya fito da wata jika sai mutumin ya daga kara, sai muka yi maza muka je; muka bincika sai muka ga kan mutun a cikin jikar.
“Da muka zagaya makabartar, mun gano kaburbura 44 babu gawarwaki a cikinsu, duk an je an yi tsafi da su; yanzu mun mika mutanen ga jami’an Amotekun.”
Majiyar ta ce daga baya jami’an tsaron Amotekun sun je sun binne kawunan a unguwar Surulere da ke garin Ondo, Jihar Ondo.
Ta ce lamarin ya auku ne a wata makabarta, mallakin wani coci a unguwar.
Kwamandan Rundunar [yankin Kudu maso Yamma] Amotekun, Cif Adetunji Adeleye ya tabbatar da tsare mutanen da ake zargin da ya ce jami’ansa sun iske mutanen unguwa na dab da aika su lahira.
Sai dai ya ce ba a samu kawunan mutane ba a tare da mutanen da aka kama kamar yadda ake zargi.
“Jami’anmu sun kubutar da mutanen da ake zargin ana dab da hallaka su, kuma mun mika su zuwa ga ’yan sanda,” inji shi.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar Ondo, Tee-Leo Ikoro ya ce ba a kawo wa Rundunar mutanen da ake zargi ba tukuna, zuwa lokacin kammala wannan rahoto.