Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta cafke wasu matasa uku da ake zargi da yin garkuwa da kananan yara a birnin jihar.
Matasan da ake zargi sun hada da Khalifa Usman, mazaunin Unguwar Kurna da Idris Aminu Sheshe da Abdullahi Aminu Sharifai.
Kakakin ’yan sanda, DSP Magaji Musa Majiya ya bayyana cewa matasan suna gudanar da wannan mummunar dabi’ar ne ta hanyar kwashe yara a unguwannin cikin birni tare da kai su yankunan da ke wajen Kano, kamar Gwarzo da danbatta da Gezawa, inda suke kai su gidajen masu unguwanni a matsayin yaran da aka tsinta, kafin daga bisani su nemi iyayen yaran su biya wasu kudi a matsayin kudin fansa, ta hanyar aika masu da katin waya.
Kakakin ya kara da cewa: “Suna kai yaran gidajen masu unguwanni ne a matsayin wurin ajiya, don kada a gane yaran suna tare da su. Idan suka sami iyayen yaran sun biya kudin da suka yi yarjejeniya, sai su gaya musu cewa su je gidan mai unguwar wuri kaza su tafi da yaronsu. Bincike ya nuna cewa sun karbi katin waya na adadin kudi masu yawa ta wannan hanyar daga iyayen yaran da suka kama. A yanzu haka an yi nasarar tserar da yara bakwai, wadanda shekarunsu suka kama daga hudu zuwa biyar daga hannun wadanda ake zargin.”
Wadanda ake zargin sun shaida wa manema labarai cewa, yawanci suna daukar yaran ne daga unwannin Kuntau da koki da kofar Mazugal da Kabuga da sauran unguwannin cikin birni, inda suke wa yaran wayo da alawa da biskit a lokutan da yaran suke dawowa daga makaranta ko kuma a kan hanyarsu ta zuwa aike.
Majiya ya ja hankalin al’ummar jihar cewa su kara kulawa da shige da ficen ’ya’yansu. Haka kuma da zarar ’ya’yansu sun fada irin wannan al’amari, su yi gaggawar sanar da hukuma. Ya kuma yi kira ga masu unguwanni da su kara lura da mutanen da ke kai masu yaran da suka bata, ta hanyar neman bayanansu da kuma sanar da hukumar ’yan sanda halin da ake ciki, don a magance wannan matsala.