Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wasu mutum biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne mazauna a unguwar Tudun Wada da ke Gombe, lokacin da suke kokarin karbar kudin fansa.
Jami’in hulda da Jama’a na Rudunar a jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ne ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gombe ranar Laraba.
- Dara ta ci gida: ISWAP ta kashe kwamandojin Boko Haram 2 a Borno
- Gwamnatin Kano ta mayar da gidan Dan Masani ‘gidan tarihi’
Yace an kama su ne a lokacin da suke kokarin karbar kudin fansa na Naira 300,000 bayan ’yan uwan wanda suka kama din sun biya Naira 100,000.
Kakakin ya ce a lokacin da suke tuhumar wadanda ake zargin, daya daga cikinsu ya ce sun sami bindiga kirar AK-47 guda uku ne suka je suka sace wani mai suna Jibrin Muhammad da ke kauyen Bantaje a jihar Taraba, sannan suka karbi kudin fansa Naira miliyan hudu.
A cewar sanarwar, binciken da suke yi ne ya sa suka yi nasarar kama daya daga cikinsu a jihar Kano wanda jami’an ’yan sandan farin kaya na Gombe suka kama.
Kakakin ya ce yanzu haka kuma suna ci gaba da bincike a kan lamarin, kuma da zarar sun kammala za su tura su gaban kotu.
Ya kuma ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ishola Babatunde Baba’ita, ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da basu hadin kai wajen sanar da su rahoton abubuwan da ke faruwa a yankunansu da sanar da duk wani motsi ko zirga-zirgar da ba su yarda da su ba ga hukumomi dan daukar mataki