Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wasu mutum masu suna Muhammadu Garba mai shekara 25 da Ibrahim Adamu mai shekara 40 da ake zargi da yin garkuwa da wani mai suna Musa Abdullahi a Gombe.
Kakakin rundunar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce a ranar 28 ga watan Satumba ne suka samu rahoton wasu mutane 14 dauke da muggan makamai da bindiga AK-47 suka shiga gidan wani mai suna Musa Abdullahi suka sace shi suka kai shi wani wajen da ba a sani ba.
Sanarwar ta ce bayan sun sace mutumin sun nemi kudin fansa Naira miliyan daya da dubu dari takwas wanda bayan sun karbi kudin kuma suka ki sakin shi.
Har ila yau ya ce wani bincike da ’yan sanda suka yi sun gano cewa wadanda ake zargin sune masu gaya wa masu garkuwa da mutane sirrin ’yan sanda.
- Sheikh Jingir ya shawarci manoma su daina sayar da kayan abinci ga masu boyewa
- Za a shiga mummunan bala’i a Gaza idan ba ku ɗauki mataki ba —MDD
Sun kuma tabbatar da cewa akwai wani mai suna Ya’u Saleh, shi ne asalin wanda ake zargi da garkuwan kuma abokin wanda aka sace din ne kuma sun hadu da wanda suka sace din kafin su sace shi suka gaya masa cewa suna shirin sace shi.
ASP Mahid ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike, da sun kammala za su gurfanar da shi a gaban kotu.