✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama malamar firamare kan yin madigo da dalibarta mai shekara 4 a Borno

Ana zarginta ne da yin madugo da yarinyar

Rundunar ’Yan Sandan jihar Borno ta kama malamar makarantar nan da ake zargi da yin lalata da wata dalibarta mai kimanin shekara hudu kacal a duniya.

Kakakin rundunar a jihar, ASP Sani Kamilu, ne ya tabbatar da kama malamar a ranar Asabar a Maiduguri.

Kamilu ya ce wadda ake zargin malama ce a wata makaranta mai zaman kanta da ke Maiduguri, kuma an kama ta ne a makon da ya gabata, inda ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

Ya ce da zarar an kammala binciken, za a mika karar zuwa ofishin kula da kararrakin jama’a (DPP) domin daukar mataki na gaba.

Mahaifin yarinyar, wanda ya kai karar ga ’yan sanda, ya ce ya lura fitsarin ’yar tasa ya canza launi zuwa ja.

“Da farko, na dauka alama ce ta kamuwa da cuta.  Na kai ta asibiti, suka gaya mana ainihin menene matsalar.

“Lokacin da mahaifiyar ta tambaye ta, sai yarinyar ta gaya mata abin da malamar ta yi mata.

“A cewar yarinyar, malamar ta rungume ta, ta ba ta nononta ta tsotsa, sannan ta sanya mata yatsa a al’aurarta.

“Mun kai rahoto ga ’yan sanda, abin da muke so shi ne a yi mana adalci,” inji mahaifin yarinyar.