’Yan sanda sun samu nasarar cafke wani da ake zargi da kwarmata bayanai ga masu masu garkuwa da mutane a Abuja.
Wanda ake zargin mai shekara 25 wanda ake yi wa lakabi da Auta na daga cikin wadanda ‘yan sandan ke zargi da jigilar makamai ga masu garkuwa da mutane da suka addabi birnin Abuja.
- A kamo jami’an lafiyar da suka ki karbar mutanen da suka yi hatsari —Zulum
- NAJERIYA A YAU: Tarihin gwagwarmayar ‘June 12’ da manufarta a dimokuradiyyar Najeriya
A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan reshen Abuja, Josephine Adeh ta fitar, ta bayyana cewa Auta na daga cikin wadanda rundunar take nema ruwa a jallo.
“Wanda ake zargin na daga cikin wadanda rundunar ke nama, an kama shi saboda hannu a jigilar makamai da harsasai da kayan abinci da muggan kwayoyi ga masu laifi a maboyarsu daban-daban da ke cikin daji ta hanyar amfani da babur.
“Kayayyakin da aka gano daga wanda ake zargin sun hada da bindigar AK47 daya, sai harsasan AK47, sai wayar salula daya da kayayyakin abinci da wani babur kirar Boxer da ba a yi wa rajista ba,” in ji sanarwar.
Haka kuma, rundunar ’yan sandan ta ce ta kama wasu mutum 12 wadanda ake zargi da kera bindigogi manya da kanana da fashi da makami da wasu laifuka.
Wadanda ake zargin wanda mafi tsufa a cikinsu shi ne mai shekaru 51 da kuma karaminsu shi ne mai shekaru 26, duka an kama su ne a yankin Zuba da ke Abuja.
Kazalika, rundunar ta ce ta kama sauran mutum takwas din a wani wurin sayar da Amala a unguwar Utako, inda har aka samu bindigogi guda uku a wurinsu da wukake da miyagun kwayoyi.