Rundunar sojin kasan Najeriya ta sanar da cewa dakarunta na Operation Lafiya Dole, sun cafke wani mai yi wa mayakan Boko Haram leken asiri a Jihar Yobe.
Ana zargin ayyukan leken asirin ne suka taimaka wajen hare-haren da ake kai wa sojoji a yankin Kamuya na Jihar Yobe.
Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa, Birgediya-Janar Mohammed Yerima ya fitar a ranar Lahadi, ta ce dakarunsu da ke Bataliya ta 27 ce suka cafke mutumin mai suna Modu Ari.
Birgediya-Janar Yerima ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mutumin yana leken asiri ne a kan ayyukan dakarun sojin da zummar kaddamar da hari a kansu ba tare da samun wata tangarda ba.
“A yanzu haka za mu ci gaba da bincike domin bankado ragowar masu taimaka masa wajen yin leken asiri a kan ayyukan dakarunmu.
“Wannan leken asiri da ake yi yana jefa dakarunmu cikin hadari musamman a yankunan Timbuktu,” a cewar sanarwar.