Rundunar ’yan sanda a Jihar Oyo ta yi nasarar kama Mista Olugbenga Asake Olusegun da ake zargin yana safarar makamai.
Ana zargin mutumin mai shekara 50 yana safarar manya da kananan bindigogi da albarusai daga wasu kasashe da yake raba wa yaransa domin aikata miyagun laifuka a sassa daban-daban na jihar da kasa baki daya.
Da yake yi wa ’yan jarida karin haske a ranar Juma’a a ofishinsa da ke birnin Ibadan, Kwamishinan ’yan sanda CP Sonubi Ayodele ya ce an kama mutumin ne a maboyarsa a cikin wani gida a Ibadan.
- MDD Ta Nemi A Gaggauta Muradun Ci Gaba Mai Ɗorewa Don Cimma Burin 2030
- Tinubu zai ƙaddamar da ayyuka a Yobe
Ya ce an gano tsabar kudi Naira miliyan 16 da bindiga kirar AK 47 guda daya da albarusai 1,346 da karamar mota kirar Toyota a tare da wannan mutumi.
Kwamishinan ’yan sandan wanda y yi wa manema labarai holen kayayyakin da aka kama, ya ce a ranar 9 ga watan Yulin da muke ciki ne asirin wannan mutumi ya tonu.
Ya ce an cafke mutumin a lokacin da jami’an rundunar da ke aikin binciken ababen hawa a birnin Ibadan suka kama wasu matasa biyu masu suna Abdulazeez Ayatullahi da Abdulazeez Ridwan a cikin wata mota ƙirar Toyota Corolla da aka gano ƙunshin alburusai a cikinta.
Kwamishinan ya ce binciken diddigi da ’yan sandan suka gudanar ne ya sa matasan suka bayyana sunan ubangidansu da ya kai ga kama shi a maboyarsa.
Olugbenga Asake Olusegun ya shaida wa ’yan jarida cewa tsabar kuɗi Naira miliyan 16 da aka samu a tare da shi ya ajiye su ne domin biyan ladan aiki ga yaransa da suke sayo masa makamai daga kasar Burkina Faso.
Aminiya ta gano cewa wadannan mutane uku na daga cikin mutane 41 da rundunar ’yan sandan ta kama da aka yi wa manema labarai holensun kan zargin aikata laifuka daban-daban a Jihar Oyo.