✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mai kera makaman ’yan bindiga a Kaduna

An kama shi ne dauke da bindigogi bakwai kirar gida da wasu kayan laifi da ya boye

’Yan sanda a Jihar Kaduna sun kama wani babban mai sayar wa ’yan bindiga makamai.

Dubun matashin mai shekaru 45 ta cika ne a kauyen Tsurutawa da ke kan hanyar Jos a Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna.

An kama shi ne dauke da bindigogi bakwai kirar gida da wasu kayan laifi da ya boye a lokacin da yake dawowa daga Jos.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, SP Mansir Hassan, ya ce daga bisani sakamakon binciken da aka yi kasa, an yi nasara kama wani abokinsa, wasu biyu kuma har yanzu ana kam neman su.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Audu Dabigi, ya yaba wa jami’an da suka yi kamen yana mai kira ga jama’a da su ci gaba da ba wa hukumomin tsaro hadin kai na sahihan bayanai domin kawar da laifuka da yaɗuwae makamai.