Kwamishinar Harkokin Mata da Walwala a Jihar Oyo, Misis Toyin Balogun, ta tabbatar da kama mutum 32 da ake zargin su da yawon barace-barace a kan hanyoyin Ibadan babban birnin Jihar Oyo.
Kwamishinar ta ce an kama su ne a dalilin karya dokar hana barace-barace a kan hanyoyi.
- Tsohon shugaban Bankin Access Herbert Wigwe ya mutu a haɗarin jirgin sama
- Jihar Zamfara na fuskantar ibtila’in cutar gubar dalma
Da take yi wa ‘yan jarida karin haske, kwamishinar ta ce, jami’an ma’aikatarta da hadin guiwar jami’an tsaro ne suka yi wannan kame a wani samame da suka kai a unguwanni daban-daban na birnin Ibadan, inda mabaratan suke yin zaman dirshan domin yin barace-barace.
Ta ce, gwamnati ta kafa dokar hana yin bara a kan hanyoyi a jihar saboda haka ya nuna takaicin yadda mabaratan suka kaurace wa matsugunin da gwamnati ta gina masu a kauyen Akinyele, inda aka tanadar masu kayan abinci da dakin shan magani domin kula da lafiyarsu, amma suka ki zama a wannan wuri sai yawon bara a kan hanya da aka haramta.
Shi ma Kwamishinan Muhalli Abdulmojeed Mogbonjubola cewa ya yi, sun gano wani mutum da ba a bayyana sunansa ba da yake aikin safarar mabarata daga garuruwan Arewa zuwa Ibadan.
Ya ce, mutumin yana can yana amsa tambayoyin jami’an ma’aikatar, kuma an yi masa kashedi ya janye daga ɗanyen aikin da yake yi.
Aminiya ta gano cewa, mabarata 32 da aka kama maza da mata da kananan yara ne da suka fito daga sassa daban-daban na Arewacin kasa, kuma dukkansu lafiyayyun mutane ne da babu wata nakasa a jikinsu.
Binciken ya nuna cewa, mutane masu lalura kamar makafi da guragu da kutare ba sa cikin wadanda aka kama domin suna zaune ne a cikin gidajensu a Unguwar Sabo mazaunin Al’ummar Hausawa a birnin Ibadan.
A lokacin da Aminiya ta ziyarci sansanin da gwamnati ta gina a kauyen Akinyele domin killace mutane masu lalura, ta samu zantawa da shugaban mazauna wannan wuri, Abubakar Atambade wanda ya ce, “gaskiya ne Kwamishina ta jagoranci kawo mutanen da aka kama domin killace su cikin wannan wuri, inda ta ja kunnen da su daina yin bara a kan hanyoyi.
Ta ce za a ci gaba da kama irin wadannan mutane daga yanzu zuwa wata 3 masu zuwa kuma duk wanda aka sake kamawa za a wuce da shi zuwa kasar Nijar ne.
Bayan tafiyar kwamishinar sai kowanne daga cikin mutanen da aka kama ya kama gabansa suka koma gidajen da suke biyan kudi a unguwar Ode-Olo da ke Inalende a Ibadan.”
Abubakar Atambade wanda shi ma yake da lalurar shanyewar kafa ya nuna takaicin ganin yadda wadannan mabarata suke bijire wa umarnin gwamnati.
Ya ce, “tun da kwamishinar ta ce akwai dokar gwamnati a kan hana yawon bara a kan titi, to kamata ya yi mu girmama doka.”
Da yake amsa wata tambaya cewa ya yi “yau shekara 3 ke nan da gwamnati ta kwaso mu daga cikin gari ta dawo da zamanmu a cikin wannan gida da muka yi wata 7 ana ba mu abinci, amma tun daga wancan lokaci sai aka dakatar da dafa mana abinci da ba mu san dalili ba.
Muna zaune ne, muna jiran samun sadaka daga bayin Allah da suke zuwa da kansu suna raba mana ‘yan kudi da abinci da sutura.