✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama mabaraciya da tsabar kudi sama da N500,000 a Abuja

Babu cikakken bayani dai a kan me matar take yi da kudin.

Hukumar kula da walwalar jama’a ta yankin Birnin tarayya Abuja ta kama wata mabaraciya da tsabar kudi har Naira 500,00 da kuma Dalar Amurka 100 a cikin buhun bararta.

Babban Daraktan Hukumar, Malam Sani Amar a yayin da ya ke tabbatarwa Aminiya faruwar lamarin a ranar Talatar, ya ce tuni aka garzaya da matar cibiyar koyar da horon sana’a ta hukumar da ke kauyen Kuciko a bayan Garin Bwari.

Ya ce an kama matar ce a Ranar Laraba da ta gabata da misalin karfe 9:00 na dare a wani karamin layi da ke Unguwar Wuse 2 Abuja, inda ta ke yin bara.

Ya ce a baya, hukumar ta taba kamata tare da koya mata sana’ar dinki  da ta zaba wa kanta a lokacin, amma sai ta tsere daga cibiyar gabanin a yayeta, sama da shekara goma kenan a yanzu.

A cewar malam Sani, sun samu nassara kamar matar ce bayan samun bayanin sirri game da ita daga wajen wani mazaunin unguwar, bayan ya tsegunta masu cewa, matar kan boye kanta a duk lokacin da ta hango tawagar motocinsu da ke yawon kame a unguwar.

“To bayan nan ne sai mu ka yi mata shiri tare da girke jami’anmu kan hanya a daren, sannan muka samu nasar kama ta.

“An wuce da ita zuwa ofishin gudanarwa na Hukumar Duba Gari ta Abuja inda aka tsareta a daren, sannan bayan wayewar gari a ka garzaya da ita zuwa cibiyar.

“A yayin binciken da a ke yi wa wadanda a ka kama ne tare da tantancesu gabanin basu mazauni a cibiyar, a ka gano kudin a cikin wani kunshi da ke tare da ita, inji shi.

“A yanzu za mu bata zabi kan sana’ar da take sha’awa kamar dinki ko tuwon gayya da zai bata yin abincin sayarwa a yayin taruka ko na yau da kullum, sannan a yi amfani da kudin wajen kama mata wurin sana’a da na jari, da dai sauransu,” inji shi.

Ya ce ce idan matar ta zaba wa kanta yin sana’ar abinci, za a saka ta a cikin rukunin mata masu girkin abinci ga al’ummar cibiyar na tsawon wani lokaci don kara gogewa.

Jami’in ya ce a baya matar ta sanar da su cewa ta yi aiki ne da wata mata da ke sana’ar abinci a Abuja, kafin ta yi fatali da aikin ta koma yawon gararanba na rokon kuxi a kan hanya.

Daraktan hukumar ya ce tuni a ka sanar da lamarin ga dangin matar inda danta ya zo daga kauyensu na Tashar-Kashin Miya da ke yankin Zariya a Jihar Kaduna, sai kuma wani wanta da da aka hada ta da shi ta waya, su ka yi magana.