✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama ma’aikacin agaji yana yi wa ’yar gudun hijira fyade

Yarinyar ta kashe kanta bayan ma'aikacin ya yi mata fyade.

Wani ma’aikacin jinkai ya shiga a hannun hukuma bayan yi wa wata yarinya ’yar gudun hijira fyade a wani sansanin ’yan gudun hijira da ke Maiduguri, Jihar Borno.

Ma’aikacin ya lalata da yarinyar ce bayan ya yaudare ta cewa za ta yi mishi aiki a gidansa Rukunin Gidajen 303 da ke kusa da Sansanin ’Yan Gudun Hijira na Dalori da ke Maiduguri a ranar Talata.

Mutumin, wanda ke aiki da wata kungiyar jin kai ta kasashen waje, yaudarar yarinyar ya yi zuwa gidansa cewa za ta yi gyara masa daki, amma ya yi amfani da damar ya zakke mata da karfin tsiya.

Da ta ka yana kokarin auka mata ne yi ta kurma ihun neman agaji, wanda hakan ya ja hankalin makwabta suka zo suka balla kofar dakin nasa suka shigo.

Da suka shigo kuma aka tabbatar cewa ya keta budurcinta, sai ta shiga dakin girkinsa a guje ta dauki wuka ta caka wa kanta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta.

Babbar Daraktan Shirin Tallafa wa Mata da Matasa ta Najeriya, Kwamred Lucy D Yunana, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce yarinyar ’yar gudun hijira ce, kuma takan yi aikin gida ne domin ta samu dan abin da take tallafa wa iyayenta da shi.

Ta ce wata kawar mamaciyar ta shaida musu a ofishin ’yan sanda cewa bayan faruwar abun, “Yarinyar ta rika kuka tana ce wa ma’aikacin, ‘Me ya sa za ka yi min haka, ka tozarta ni, ka keta buturcina, ka ja wa iyayena abin kunya? Ni da in kai wa iyayena wannan abin kunya gara na mutu.”

Wani dan sanda, ya tabbatar wa wakilinmu cewa an tsare ma’aikacin kungiyar agajin a caji ofis din da ke Gwange, daga baya a ranar Laraba aka wuce da shi zuwa Babban Ofishin ’Yan Sanda Masu Binciken Manyan Laifuka da ke Jihar.
%d bloggers like this: