Jami’an ’yan sanda sun kama wani limamin masallaci da kokon kan mutum a Unguwar Iwo da ke cikin jihar Osun.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Wale Olokode ne ya tabbatar da hakan bayan kama wanda ake zargin dauke da shaidar tabbatar da abin da ake zargin sa da aikatawa.
- Iyaye sun yi karar saurayin ’yarsu kan fasa auren ta
- An nada kanin Kwankwaso sarautar Makaman Karaye
- Kannywood ta zama kasuwar bukata – Zango
- An kai daraktan Kannywood Ashiru Nagoma asibiti
Wanda ake zargin, an mika shi ga hedikwatar ofishin rundunar ’yan sanda ta Iwo daga nan za a wuce da shi zuwa Cibiyar Binciken Laifuka ta Jihar da ke Osogbo babban birnin jihar don zurfafa binciken wanda ake zargin.
A wata tattaunawa da aka yi da limanin a hedkwatar ’yan sandan ya amsa laifin kawo kan mutum kan Naira dubu 20 daga wajen abokinsa.
“Tabbas an kama ni ne da kan mutum. Na siyo ne daga wajen wani, zan yi amfani da shi ne wajen yin tsafin mallakar kudi.
“Na sayi kan ne a kan Naira dubu 20,” inji.
CP Olokode ya ce an kama wasu da ake zargi da hannu kan lamarin, sannan za a mika su ga kotu bayan yi binciken.