✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama likita bisa zargin sace jariri a Abuja

An kama likitan bayan bore daga mazauna yankin wanda ake zargin ba shi ne karo na farko ba.

’Yan sanda na gudanar da bincike a kan bacewar wani jariri, sa’o’i kalilan bayan haihuwarsa a wani asibiti mai suna Trendy Hospital Clinic and Maternity da ke Unguwar Dutse Makaranta, a Karamar Hukumar Bwari a Abuja.

An kama likitan ne tare da rufe asibitin nasa a ranar Lahadin da ta gabata, bayan bore daga mazauna yankin a kan lamarin, wanda ake zargin ba shi ne karo na farko ba.

Mahaifiyar jaririn mai suna Favour Idowu mai shekara 17, an garzaya da ita wani asibiti da ke yankin, inda take samun kulawa.

A zantawarta da Aminiya, ta ce ta ziyarci likitan a ranar Larabar makon jiya a kan matsalar murdar ciki da ya addabe ta.

Ta ce, “Ya ba ni kwayar magani da ya umarce ni da na saka a karkashin harshena, sannan ya cusa min wani a cikin al’aurata.

“Bayan wani lokaci sai na fara jin nakuda da ya ci gaba da murdewar ciki har zuwa ranar Asabar lokacin da na haihu.

“Ya bugi jikin yaron inda ya yi kuka, ba ajima ba sai na suma, daga baya bayan na farfado sai na ga jariri a kusa da ni.

“Bayan wani lokaci sai wasu mata biyu suka fita da yaron. Likitan ya shaida mini cewa za su yi masa riga-kafi ne, shi ne ganin karshe da na yi wa yaron, bayan na farka ne sai na gan ni a wannan asibitin na yanzu,” inji Favour.

Ta kuma musanta zargin da ake yi kan akwai yarjejeniyar likitan zai ba ta wani kudi, kuma kasancewa an fuskanci akasi a lamarin ne, maganar ta kai ga ’yan sanda.

Ta yi korafin cewa, wanda ke da alhakin yi mata cikin, ya musanta lamarin tun a watannin farko na cikin.

Wani dan uwan mahaifiyar jaririn mai suna Samuel Idowu, ya ce, sun shigar da kara a gaban ’yan sanda a kan lamarin sannan daga bisani aka samu nasarar kama likitan.

Ya ce, ’yar uwar tasa ta dawo hayyacinta ne bayan ta shafe kwana biyu a sabon asibitin da a kai ta, inda take ci gaba da zaman jinya har zuwa shekaran jiya Laraba.

Wani mai makwbtaka da asibitin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, kamar mako uku gabanin faruwar lamarin, an ji wata mata tana rigima da likitan kan alkawarin yaro da ya yi mata ba tare da cikawa ba.

Haka kuma wata majiya ta ce, an kama wata mazauniyar yankin Arab road da ke garin Kubwa a ranar Litinin da ta gabata a kan wani al’amari da ke da nasaba da kama likitan.

Babban jami’in ‘yan sanda na Dutsen-Alhaji, CSP Paul Danladi ya tabbatar da faruwan lamarin.

Ya ce, an kama wadanda ake zargin, sannan ana neman wani saurayin uwar jaririn mai suna Joseph da ake zargi da kai ta wajen likitan sannan ya karbi Naira dubu dari hudu ya gudu.

Ya ce, an mika karar zuwa Rundunar ‘yan sanda ta Abuja don ci gaba da gudanar da bincike a can, kasancewar iyalan da jaririn ke hannunsu sun shigar da kara kan lamarin a can.