✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama Lakurawa sun kai wa ’yan sanda sanda hanci

Sun je da maƙudan kuɗaɗe da suke son bayarwa cin hanci ga babban jami'in binciken ’yan ta’addan

’Yan sanda sun kama wasu mutane uku da suka kai musu cin hanci domin hana binciken mayaƙan Lakurawa da aka kama a Jihar Kebbi.

Mutane ukun da ake zargin shan sa alaƙa da Lakurawa sun shiga hannu ne baya sun je da tsabar kuɗi Naira miliyan 1.6 da suke son bayarwa cin hanci ga babban jami’in da ke binciken ’yan ta’addan.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, ya sanar a ranar Talata cewa mutanen su uku sun nemi  su ba sa kuɗin ne domin ganin jami’an ’yan sandan sun shiriritar da bincike da kuma kuma gurfanar da Lakurawan.

Ya ce, “Nan take aka tsare su aka kulle, inda aka fara bincike a kansu,” in ji SP Abubakar.

Ya jaddada aniyar Kwamishinan ’yan sandan jihar, Bello M. Sani, na yaƙar manyan laifuka da ta’addanci.

Sannan ya ba wa al’ummar jihar tabbacin yin mai yiwuwa wajen samar da tsaro da zaman lafiya domin samun bunƙasar tattalin arziki.