✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama Kansila mai ci da AK-47 kusa da sansanin masu garkuwa da mutane

An kama shi ne lokacin da yake kokarin kai musu bindigar

’Yan sanda a Jihar Kaduna sun cafke wani Kansila mai ci da bindiga kirar AK-47 a garin Galadimawa da ke Karamar Hukumar Giwa da ke Jihar.

An cafke Kansilan ne a kan babur lokacin da yake kokarin kai bindigar ga wani da ake zargi yana maboyar ’yan bindiga ne a yankin.

Rahotanni sun yi ce Kansilan Mai suna Abdul Adamu Kinkiba ya ce wani ne ya ba shi bindigar ya kai wa wani.

Sai dai ya ce bai san sunan wanda ya aike shi da bindigar ba kuma bai san wanda zai kai wa bindigar ba.

“Ni dai an ce da na haye gadar Galadimawa ba tsaya, mutumin zai fito ya karba,” a cewar shi.

A zantawar mu ta wayar tarho da Shugaban Karamar hukumar Soba, Injiniya Suleiman Yahaya Richifa ya tabbatar da cewa Abdul Adamu Kinkiba wanda ake zargin zababben kansila ne a majalisar Karamar Hukumar.

Ya ce, “Labarin ya ruda ni, kuma ya sa na shiga wani irin halin jimami. Don Allah ku kyale ni. Babu abin da zan kara maku daga nan,” inji Shugaban.

Tuni dai Aminiya ta gano cewa jami’an ’yan sanda suka yi awon gaba da wanda ake zargin zuwa hedkwatar rundunar ’yan sanda da ke Kaduna don ci gaba da bincike.

Aminiya ta tuntubi Kakakin rundunar ’yan sanda Jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ta wayar salula amma ya ce a ba shi ’yan mintuna zai kira daga bisani.

Sai dai har zuwa lokacin hada rahoton bai kira ba.