✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama jarkokin fetur 2200 yayin fita da su kasar waje

Rundunar Kwastam ta Seme a kan iyakar Najeriya da kasar Benin ta yi nasarar kama jarkoki (lita 25) guda 2200 cike da man fetur da…

Rundunar Kwastam ta Seme a kan iyakar Najeriya da kasar Benin ta yi nasarar kama jarkoki (lita 25) guda 2200 cike da man fetur da nufin yin fasa kwaurinsu zuwa kasar Benin da ke makwabtaka da Najeriya.

Da yake nuna wadannan jarkoki da aka baje kolinsu a harabar ofishinsa, Kwamandan Rundunar Kwastam ta Seme, Kwanturola Muhammed Aliyu ya ce “mun kama wadannan jarkoki ne a cikin dare a ranar Juma’a da ta gabata, a kauyen Owode-Apo a kan hanyar Badagry a kusa da kan iyakar Najeriya da Benin da aka yi lodinsu a cikin kwale-kwale da nufin satar ficewa da su zuwa wata kasa ta cikin ruwa.”

Ya ce, “lita dubu 55 ne a cikin jarkokin da muka kama da darajar kudinsu ya haura Naira miliyan 10 kuma ba mu kama kowa a kan wannan al’amari ba, domin mutumin da ya mallaki kayan ya gudu ya bar ladansa a lokacin da jami’an Kwastam da hadin gwiwar sojoji suka yi wa dajin dirar mikiya.”

Ya karyata rade-radin cewa manyan motocin tanka dauke da man fetur suna bi ta kan iyakar Seme, suna ficewa zuwa wata kasa. Ya ce, “wannan ba gaskiya ba ne, domin babu motar tanki da ta isa ta tsallake shingen da muka shimfida a kan iyakar Najeriya domin kare mutuncin kasa.”

Ya yi karin haske cewa, “abin da ke faruwa shi ne, irin wadannan mutane da suka mallaki lasisin gidajen sayar da mai na kashin kansu suna dauko man fetur, su ajiye a gidajen mai da suka mallaka idan dare ya yi sai su juye cikin jarkoki. Irin wannan bayani da muka samu a boye shi ne ya kai ga nasarar yin wannan kame da ba a taba yin irinsa ba. Kuma za mu ci gaba da yin irin wannan aiki sai mun ga abun da ya ture wa buzu nadi.”

Dangane da abin da suke shirin yi da wannan man fetur sai ya ce, “irin wanda muke kamawa a baya ba mai yawa ba ne, muna sayar da shi ne ga mabukata a nan Seme. Amma a yanzu saboda yawan wannan da muka kama ba za mu sayar a nan ba domin guje wa yin aikin baban giwa, da za a saya a sake yin wani yunkurin fita da shi zuwa wata kasa. Shi ne ya sa muka yanke shawarar mika shi ga ofishinmu na FOU da ke Ikeja a Legas su sayar wa jama’a a can.”

Kwanturolan ya lissafo wasu muhimman abubuwa da rundunar ta yi tanadi domin dakile ayyukan fasa kwauri cikin wannan shekara, da suka hada da gyaran na’urar daukar hoton kaya mai gani har hanji, wadda take bankado dukkan kayan da aka boye domin shigowa da su cikin kasa ta haramtacciyar hanya. Haka kuma “akwai aikin koyon harbin bindiga da jami’an Kwastam suke samu daga sojoji da zai taimaka mana wajen fuskantar masu yin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya.”