’Yan sanda a Jihar Legas sun kama wasu jami’an tsaro da ’yan daba har su 15 da ake zargi da karbar haramtattun kudade a hannun direbobin manyan motoci kafin a kyale su su wuce.
Rundunar ta kama su ne ranar Juma’a yayin wani samame da ta kai.
- NAJERIYA A YAU: Bazatan Ministocin Tinubu ga ‘Yan Najeriya
- Sojojin Nijar sun yi kunnen uwar shegu da wa’adin ECOWAS
Daga cikin mutanen da aka kama har da ’yan sanda 3 da na kiyaye hadura (FRSC) da kuma na LASTMA.
Da yake yi wa ’yan jarida bayani a kan lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce wani sashe na musamman a karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legas, CP Idowu Owohunwa ya nada ne ya gudanar da aikin kama mutanen.
Ya ce an kama su ne a kan babbar hanyar Mil 12 da ke birnin Legas.
Da yake nuna mutanen da aka kama a wajen taro da ’yan jarida a hedkwatar rundunar da ke Ikeja, SP Benjamin Hundeyin ya ce Kwamishinan ya damu kwarai da yawan koke-koken yadda ’yan daba suke tare hanyoyi da tilasta karbar haramtattun kudade daga hannun direbobin kafin su kyale su su wuce.
Ya ce dalili ke nan da Kwamishinan ya dauki matakin kafa sabon sashe da ya kunshi jami’an ’yan sanda na musamman da zai rinka gudanar da aikin dakile mummunan aikin da ’yan-daban ke yi a kan hanyoyin Jihar.
Kakakin ya ce Kwamishinan ya ja kunnen masu aikata irin wannan danyen aiki su tattara nasu ya nasu daga kan hanyoyin Jihar ko su fuskanci fushin rundunar.
Ya tabbatar wa direbobin abubuwan hawa a Jihar cewa sabon sashen da aka kafa a kan wannan lamari zai yi aiki ka’in da na’in wajen kawar da irin wadannan mutane da suka dade suna cin karensu ba babbaka a kan hanyoyin Jihar.