✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama jagoran ’yan sa-kai da suka kai hari ana bikin sallah a Zamfara

Sun yi wa jama’ar kauyen da suka kaiwa hari ikirarin cewa murnar bikin sallah suke yi.

’Yan sanda sun kama wani fitaccen jagoran haramtacciyar kungiyar nan ta ’yan sa-kai da ake zargi da kai hari ana tsaka da shagulgulan bikin sallah a Jihar Zamfara.

Rundunar ’yan sandan ta bakin kakakinta na Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ta ce sun kama Bala Minister da ake zargin ya kitsa harin da aka kai kauyen Tungar Dutsi da ke Karamar Hukumar Bukkuyum a ranar Talata, 3 ga watan Mayu wanda ya yi daidai da rana ta biyu ta shagulgulan bikin Karamar Sallah a bana.

SP Shehu ya ce ana zargin Bala Minister, wanda shi ne jagoran haramtacciyar kungiyar ’yan sa-kai a kauyen Tungar Bido da jagorantar harin da aka kai kan al’ummar Tungar Dutsi a gundumar Gada.

A cewarsa, Bala Minister da yaransa sun kai harin ne da bindigogi kirara gida da wasu makamai masu hatsari, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

“Sun yi wa jama’ar ikirarin cewa murnar bikin sallah suke yi, inda bayan wasu mazauna kauyen sun nuna rashin jin dadinsu a kan hakan, sai suka fara harbe-harbe.

“Sun kuma farmaki wasu mutanen kauyen da wukake, adduna da sauran makamai masu hatsari.

“Ana tsakar haka ne suka kashe wani Surajo Ali mai kimanin shekaru 40, kuma nan da nan muka cafke jagoran maharan yayin da ragowar suka tsere,” a cewar SP Shehu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito SP Shehu yana cewa, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun cafke ragowar masu hannu a harin domin su fuskancin fushin doka.