✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama hodar Iblis a boye a injin jirgin ruwa a Legas

An gano hodar Iblis mai nauyin kilogram 32.9 da ma'aikatan jirgin suka boye.

Jami’an taron hadin gwiwa sun cafke wani jirgin ruwan dakon sukari dauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 32.9 a Jihar Legas.

Bayan binciken da jami’an tsaron suka gudanar, sun gano yadda ma’aikatan jirgin suka boye hodar iblis din a cikin injin din jirgin din ruwan.

An cafke jirgin da ke dauke da hodar Iblis din ne a yayin da yake kokarin ficewa daga Jihar Legas.

Jami’an tsaron da suka da dakarun sojin ruwa da Kwastam da ’yan sandan kasa da kasa da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), sun tabbatar da kama jirgin mai suna MV CHAYANEE NAREE a ranar Alhamis.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto, ana ci gaba da loda sukari a cikin jirgin, amma babu tabbacin za a bari jirgin ya tashi ko kuwa.