An kama mai ba Gwamnan Jihar Nasarwa Shawara kan Ababen more rayuwa da wasu ’yan kasar China bisa zargin satar karafan titin jirgin kasa.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta cafke hadimin gwamnan ne tare da wasu ’yan kasar China biyu kan saye da sayar da karafa da takalmin layin jirgin kasa na sata.
Ta ce daya daga cikin ’yan kasar Chinan shi ne Manajan kamfanin sarrafa tama na Yong Xing da ke Abuja, yana kuma sayen kayan titin jirgin kasan da aka sato.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, Bola Longe, ya ce jami’an ’yan sanda biyu da wani jami’in hukumar tsaro ta Sibil Difens da wani tsohon Kansila na daga cikin wadanda aka kama kan badakalar karafan titin jirgin kasan.
Ya ce an kuma kama lauyan kamfanin Yong Xing kan yunkurin bayar da cin hancin Naira dubu 600 domin a saki mai gidansa dan kasar Chinan.
Amma a zantawarsa ta musamman da wakilinmu, mai ba gwamnan shawara ya ce ba shi da masaniyar cewa kayan da aka sayar masa na sata ne.
“Ni dan kasuwa ne da ke harkar saye da sayarwa, har da na kayan gwangwan, ina kuma da ejen da ke kawo min kaya kuma na yarda da shi.
“Shi ne ya sayar min da kayan, amma ya rasu a watan da ya gabata a kan hanyar Akwanga zuwa Nasarawa Eggon.
“Karon farko ke nan da suka kawo min karafa da takalman titin jirgin kasa in saya, na kuma sayar Naira miliyan 3.6,” inji shi.
Bola Longe ya gabatar da su ne a ranar Alhamis a cikin wasu mutum 66 da ake zargi da ayyukan fashi da garkuwa da mutane a Kananan Hukumomin Lafia da Keana na Jihar.