✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama Fasto kan zargin fashi da makami

Wani Fasto a Legas ya shiga komar ’yan sanda bisa zarginsa da da laifin fashi da makami. Asirin faston mai suna Daniel Onwugbufor ya tonu…

Wani Fasto a Legas ya shiga komar ’yan sanda bisa zarginsa da da laifin fashi da makami.

Asirin faston mai suna Daniel Onwugbufor ya tonu ne a sakamakon tsaurara bincike da rundunar ’yan sanda bangaren SARS a Jihar Ogun ta yi, a ƙarƙashin jagorancin Uba Adams, bayan da rundunar ta samu bayanan yawaitar fashin manyan motoci a tsakanin jihohin Legas da Ogun.

A cewar Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun, ASP Abimbola Oyeyemi, rundunar ta yi nasarar kame faston ne bayan da suka yi amfani da hanyar kimiyya suka gano wata mota ƙirar Jeep a gidansa da ke Unguwar Iba, motar da aka yi fashinta da manyan bindigogi a yankin Aja Legas. “Kame faston ne ya ba mu damar kama ƙarin mutum guda a cikin ’yan fashin mai suna Animashaun, wanda ya shaida mana cewa shi da ƙarin abokan ta’asarsa mutum biyu suka yi fashin motar, inda suka kai wa faston ya kuma ba su Naira dubu 350 kacal. Ya ce faston ne yake sayar da kayan satar da sukan yiwo fashinsu, domin a baya ma sun sato babbar wayar salula ta Samsung Galady amma sai ya saye ta a Naira dubu 35,” inji shi.

Abimbola ya ce tunda farko, faston ya musanta cewa yana da masaniyar Animashaun ɗan fashi da makami ne, sai dai daga baya ya amsa laifinsa, ya ce ya riga ya tura motar da suka sata garin Anaca, inda a can ne yake tura motocin a sayar masa. Ya kuma sha alwashin bai wa ’yan sandan haɗin kai har a kai ga gano motar tare da kame ragowar masu hannu a fashin.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun Ahmad Iliyasu ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ’yan sandan za ta kamo ragowar ’yan fashin tare da hukunta su kamar yadda dokar ƙasa ta tanada. Ya kuma shawarci al’ummar jihar su zamo masu sanya ido tare da ankarar da rundunar da bayanai. Ya ce hakan zai ba da damar kawar da ɓatagari a jihar.