’Yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike kan wani limamin coci da dansa da ake zargi da kashe wata buduruwa da kuma daddatsa sassan jikinta a garin Kubwa da ke yankin a Babban Birnin Tarayya Abuja.
A ranar Litinin da ta gabata ce mazauna garin na Kubwa suka wayi gari da mummunan labarin bayan an gano wata jaka da a ka jefar a wani juji da ke da kusa da gadar P.W da ke garin.
- Yan bindiga sun sace matar soja da wasu mutum 6 a Kaduna
- Me Dokar Zabe ta ce kan canza ’yan takarar ‘wucin gadi’?
Wani mai sana’ar gadi a daya daga cikin wuraren kasuwanci da ke da kusanci da wajen, ya shaida wa Aminiya cewa matasa masu sana’ar kwasar shara da a ka fi sani da ’yan bola ne suka fara gano buhuna ukun da a ka sanya sassan jikin budurwar a ciki, sai kuma mushen akuya da na kare da a ka zuba a cikin ragowar buhunan.
Bazuwar labarin ke da wuya, sai wani mai sana’ar tukin babur mai kafa uku ya kai kansa gaban ’yan sanda tare da shaida masu cewa shi ne ya dauki buhunan uku da kuma dan faston zuwa inda jujin yake.
Ya ce ya dauke su ne a daren Lahadin da ta gabata da misalin karfe tara na dare, inda a cewarsa, mutumin ya sanar da shi cewa wasu abubuwa ne marasa amfani da ya ke so ya zubar.
Majiyar ta ce matashin ya dauko mai babur din ne daga mashigar unguwar Bazango, inda suka saba tsayawa don daukan fasinja, tare da bukatar ya bi shi zuwa majami’ar don daukan kayan, inda ya biya shi N1,000.
“Mai sana’ar tukin babur din ya kuma taimaka wajen kai ’yan sanda zuwa majami’ar a ranar ta Litinin da misalin karfe 3:00 na rana, inda a ka sami nasarar samun matashin a wani bangare na majami’ar.
Wakilinmu ya zanta da wasu mazauna unguwar da majami’ar ta ke, inda suka ce sun ga lokacin da ’yan sanda suka fito da matashin daure da ankwa a hannayensa, sannan suka tisa keyarsa zuwa cikin motarsu tare da shi kansa Faston da ke matsayin mahaifinsa.
Baturen ’yan sanda (DPO) na Kubwa, CSP Abubakar Abdulkarim, wanda ya tabbatar da faruwan lamarin, ya ce ana ci gaba da bincike a kan mutum biyun, a yayin da a ka ba da ajiyar sassan jikin matashiyar a dakin ajiyar gawa na Asibitin Kubwa.
Aminiya ta gano cewa ’yan sandan sun sake komawa cikin majami’ar a ranar Talata don gudanar da bincike tare da rufe wajen.
Sai dai tuni a ka bude majami’ar kamar yadda wakilinmu ya shaida a yayin ziyarar zuwa wajen a safiyar Laraba, inda a ka ga wasu yara biyu suna zaune a cikin wani shagon kayan masarufi, da ke hade da majami’ar.