✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dillalan bindigogi a Kaduna

Wani dillalin bindigogi ya shiga hannu a jihar Kaduna inda ‘yan sanda suka kwace bindigogi 43 tare da tsare masu garkuwa da mutane da ’yan…

Wani dillalin bindigogi ya shiga hannu a jihar Kaduna inda ‘yan sanda suka kwace bindigogi 43 tare da tsare masu garkuwa da mutane da ’yan fashi da sauran masu manyan laifuka.

’Yan sandan sun kuma kwace bindigogi 18 a hannun wani makerin bindigogi suka kuma kwace albarusai 1,113, daga wurin masu aikata manyan laifuka guda 207 da suka gabatar a ranar Laraba, cikinsu har da masu fyade guda 81.

“Ina sayar da harsasan da nake samowa a wurin wani mutun N500 kowane guda daya ga wasu mutane a nan Rigasa”, inji dillalin makaman a zantawarsa da ‘yan jarida.

Shi kuma makerin bindigon ya ce bai kai ga sayarwa ba kuma ya gaje su da kuma sana’ar ne daga kakansa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Umar Muri ya ce sun kwace manya da kananan bindigogi 43 da kuma tsabar kudi Naira miliyan 93 da Riyal 180,000 na kasar Saudiyya daga hannun wadanda ake zargin.

Sun kuma kwace takardun jabun kudade na Dalar Amurka 5,700,000 da Yuro 210,000 da Sefa 2,700,000 da kuma Naira 8,650,000.

Sauran kayan da aka kwato sun hada da shanu 833 da buhu 48 na tabar wiwi da layu da dai sauransu.

’Yan sandan sun kuma shawarci jama’a da su yi hattara saboda yawaitar takardun kudade na bogi a hannun ’yan damfara baya ga masu tura wa mutane sakon banki na karya.